John Terry: Ba za ni wata kungiya ba

Hakkin mallakar hoto v
Image caption Abubuwa sun sauya yanzu kungiyar ce ke da iko inji Terry

John Terry ya ce yana fatan ci gaba da zama a Chelsea na wasu 'yan shekaru, kuma babu wata kungiya da zai yi wa wasa.

Kyaftin din wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar wasan nan, shi ne ya fara ci wa kungiyar kwallonta a wasan karshe na kofin Capital One, da suka doke Tottenham 2-0 a Wembley.

Ya ce, ''idan wannan ita ce shekarata ta karshe, ina fatan za ta kare da gagarumar nasara.''

''Amma kuma ina jin dadin ci gaba da wasana, kuma ina ganin bai dace ba in tafi yanzu.''

Da aka tambaye shi ko zai koma wata kungiyar, dan wasan mai shekara 34, ya jaddada cewa, a'a.

Tsohon kyaftin din na Ingila ya ce, ''ina da dan burin wasa a shekara mai zuwa, amma kuma bayan nan, shekara biyu ko uku, ban san abin da zai biyo baya ba.''

Chelsea na da ka'idar bai wa 'yan wasan da suka wuce shekara 30 kwantiragin watanni 12.

Kungiyar wadda za ta je gidan West Ham ranar Laraba, ita ce kan gaba a Premier da tazarar maki biyar, yayin da ya rage wasanni 12 a kare gasar.

Sai dai tana da kwantan wasa daya da ba ta yi ba da Manchesterr City, wadda ke matsayi na biyu.