Skrtel zai buga wasanmu na gaba - Rodgers

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Skrtel ya suma a cikin fili

Martin Skrtel zai iya murmurewa har ya buga wasan Liverpool tsakaninta da Swansea a gasar Premier ta Ingila duk da cewa ya suma a wasansu da Blackburn na cin kofin FA.

Skrtel mai shekaru 30 ya fadi da kai cikin mintuna uku da soma wasan.

Bayan an dakatar da wasan na mintuna takwas, an dauki dan wasan a makara amma kocinsa Brendan Rodgers ya ce "Ya samu sauki, ya nemi ya ci gaba da buga kwallon bayan nan."

"Ina tunanin zai iya buga wasanmu na gaba," in ji Rodgers.

A yanzu Liverpool ce ta biyar a kan teburin gasar Premier inda take da maki 51 cikin wasanni 28.