Mancini na son Yaya Toure

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A shirye nake na kawo Yaya Toure Inter Milan

Tsohon kociyan Manchester City Roberto Mancini ya ce ya yi amanna Yaya Toure yana son barin kungiyar, kuma a shirye yake ya dauke shi a Inter Milan.

Shekara biyar ke nan dan wasan na Ivory Coast mai shekara 31 yana Man City.

Kuma ya dauki Premier League lokacin Mancini a 2012.

Mancini wanda yake tare da Inter Milan tun watan Nuwamba ya ce ya yi wasa a kowace gasa (league) in ban da ta Jamus da Italiya.

Toure wanda ya taimaka wa Ivory Coast ta dauki kofin Afrika a watan da ya wuce, ya fara kwallonsa ta kwararru a Beveren ta Belgium.

Haka kuma ya yi wasa a Ukraine da Girka da Faransa kafin ya je Barcelona a 2007.

Ya dauki kofin Zakarun Turai da kofin duniya na kungiya da kofin zakaran zakaru na Turai(Uefa Super Cup0 da na La Liga biyu da kuma Copa del Rey a shekara uku da ya yi a Nou Camp.