Zakarun Turai:Real Madrid ta sha da kyar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ronaldo ya ci biyu Benzema ya ci daya

Real Madrid ta kai wasan dab da na kusa da karshe na kofin Zakarun Turai da kyar bayan ta yi nasara kan Schalke da ci 5-4 gida da waje.

A karawar da aka yi Talatar nan Schalke ta yi nasara a kan Real Madrid da ci 4-3, sai dai tun a wasansu na farko a Jamus Real ta ci su 2-0.

Saboda haka jumulla Real Madrid ta yi galaba da ci 5-4 ke nan.

Real ta samu zuwa wasan dab da na kusa da karshe (quarter finals).

A daya wasan na Talatar, Porto ta kai wasan dab da na kusa da karshen bayan ta yi galaba a kan Basel 5-1 jumulla.

A wasan na Talata Porto ta zura kwallo hudu ba ko daya a ragar Basel.

A wasansu na farko a gidan Basel( Switzerlan) sun ta shi 1-1.