Welbeck: Ban san na yi murnar cin United ba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Welbeck yana murnar cin Manchester United

Danny Welbeck wanda ya yi burede lokacin da ya ci tsohuwar kungiyarsa Manchester United, a wasansu na kofin FA, ya ce, ba zai iya tunawa ya yi murnar ba.

Kwallon da Welbeck ya ci Man United a minti na 61,wadda ita ce ta Arsenal ta biyu bayan ta Nacho Monreal, ita ta fitar da United din daga gasar ta kuma kai Arsenal wasan kusa da karshe.

Dan wasan na Ingila ya kara da cewa,''a ko da yaushe ina mutunta magoya bayan kungiyar, sun yi min kyakkyawar tarba kuma na gode da hakan.''

Welbeck wanda y shiga Man United tun yana shekara takwas, ya kar da cewa,'' Manchester United kungiya ce da ke da muhimmanci sosai a wurina, ina kaunarta.''

A rana ta karshe ta saye da sayar da 'yan wasa a watan Satumba kociyan United Louis van Gaal ya sayar da Welbeck a kan fan miliyan 16, saboda wai ba ya cin kwallo sosai.

Kociyan ya maye gurbinsa da Radamel Falcao wanda ya zuwa yanzu kwallaye hudu kawai ya ci, yayin da shi kuma Welbeck ya ci wa Arsenal takwas.