Wariyar launi: An yi watsi da kyautar Chelsea

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutumin ya ce ba za a iya saye shi da 'yar guntuwar takarda ba

Bakar fatan nan dan Faransa da magoya bayan Chelsea suka ci mutuncinsa ta wariyar launin fata wajen hana shi shiga jirgin kasa a Paris ya yi watsi da tikitin shiga kallon wasansu kyauta da kungiyar ta ba shi.

Chelsea ta ba shi kyautar tikitin ne domin kallon wasan da za su sake karawa da PSG a London ranar Larabar nan.

Souleymane S, mai shekar 33 ya shaida wa wani gidan rediyo na Faransa cewa har yanzu yana cikin damuwa game da lamarin.

Mutumin dan asalin kasar Mauritania wanda kuma dan Faransa ne ya ce ba za a iya saye shi da wata yar guntuwar takarda ba.

Za a gurfanar da mutane biyar da ake zargi da aikata laifin a kotun Majistare ta Waltham Forest ranar 25 ga watan Maris, bisa tuhumar hukumar 'yan sandan London.

Lamarin na nuna wariyar launin fatar ya faru ne kafin wasan Chelsea da PSG a watan Fabrairu.