Zakarun Turai: Ancelotti ya nemi afuwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Carlo Ancelotti ya ce ba za su bayar da kofar da za ta sa kimarsu ta ragu ba

Kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti, ya nemi afuwa saboda gazawar kungiyarsa a wasan da ta buga da Schalke, yana mai cewa sun cancanci dukkanin sukar da aka yi musu.

An yi wa kungiyar ta Real Madrid, wacce ke kare kambunta na gasar cin Kofin Zakarun Turai, ihu a Bernabeu bayan Schalke ta doke su da ci 4-3.

Sai dai duk da kashin da suka sha, Real ta kai wasan dab da na kusa da karshe saboda tun a wasansu na farko a Jamus Real ta ci Schalke 2-0.

Don haka a jumlace, sun tashi da ci 5-4 gida da waje.

Magoya bayan kungiyar dai sun yi ta daga musu kyalle, wato abin da ke nuna kyamarsu bisa gazawarsu.

Sai dai Ancelotti ya ce,"Ina neman afuwa. Mun gaza a wasan da muka yi kuma hakan ba girmanmu ba ne."

Ya kara da cewa,"Mu kwararru ne, ba za mu bayar da kofar da za ta sa kimarmu ta ragu ba."