Twitter: FA ta ci tarar Cole fan 20,000

Hakkin mallakar hoto
Image caption Dan wasan ya amsa laifinsa na saba dokar hukumar

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, ta ci tarar dan wasan West Ham, Carlton Cole fan 20,000 kwatankwacin naira miliyan shida saboda zagin mai goyon bayan Tottenham a Twitter.

Haka kuma hukumar ta gargadi Cole mai shekara 31 da ka da ya sake wani abu makamancin haka.

Tun da farko dan wasan ya amsa laifinsa na saba dokar hukumar.

Tsohon dan wasan na Ingila ya aika wa da mai goyon bayan Tottenham din maganganu na batanci a shafinsa na Twitter bayan wasansu na watan da ya gabata da suka yi 2-2.

A watan Afrilu na 2011 ma an ci tarar dan wasan fan 20,000 saboda kalaman da ya rubuta a Twitter a lokacin wasan sada zumunta tsakanin Ghana da Ingila.

A kakar bana Cole ya buga wa West Ham wasanni 17 inda ya ci musu kwallo uku.