Chamberlain zai yi jinyar makonni hudu

Image caption Chamberlain ba zai buga wasa ba har tsawon makonni 4

Kocin kulob din Arsenal Arsene Wenger, ya ce an dakatar da dan wasansa na gefe Alex zai yi jinyar makonni 3 zuwa 4, sakamakon raunin da ya ji a gwiwa.

An ji wa dan wasan mai shekara 21 rauni ne a karshen makon da ya wuce .

"Abin takaici ne. Abin kunya ne a ce a baya nan a daidai lokacin da ake bugun karshe," in ji Wenger.

Wasannin da Oxlade-Chamberlain ba zai buga ba sun hada da wasan da Ingila za ta kara da Lithuania a wasan neman cancantar shiga gasar kasashen Turai ta 2016 ranar 27 ga watan Maris da kuma wasan sada zumunci da za a buga tsakanin Ingilan da Italiya kwanaki 4 bayan wancan.

"A ranar Litinin da daddare ne ya nuna gwanintarsa in da mu ka ga matukar muhimmancinsa ga Arsenal da Ingila," A cewar Mr Wenger.

Kocin ya kara da cewa dan wasan baya Gabriel ya dawo filin bayas da horo bayan raunin da ya ji a gwiwa lokacin da suka kara da QPR ranar 4 ga watan Maris.