'Chelsea ce za ta yi nasara a gasar Premier '

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan Chelsea na murnar samun nasara a wasa

Kocin Chelsea Jose Mourinho, ya yi hasashen cewa kungiyarsa ce za ta lashe gasar Premier ta wannan kakkar wasannin.

A cikin makon nan ne dai kungiyar Paris St-Germain, ta doke Chealse a gasar zakarun turai, amma kuma ita ke kan gaba da maki biyar a saman teburin gasar Premier a yayinda ya rage wasanni 11 a kamalla gasar.

Mourinho ya ce: "Mutanen da aka ci su wasa ranar Larabar da ta gabata, su ne dai kuma mutanen da ke kan gaba a gasar tun ranar farko da aka farata."

"Su ne kuma mutanen da su ka yi nasarar lashe kofin Capital One kuma su ne dai za su yi nasara a gasar Premier," in ji Mourinho.

Mourinho ya ce ya yi wani taro da 'yan wasansa domin tattauna shan kashin da suka yi lokacin da suka dauki bakuncin kungiyar PSG a gasar zakarun turai.

Ina ya kara da cewa "kuma yanzu na rufe maganar."

Ya kara da cewa: "Abin da kawai zan yi magana a kansa dangane da gasar zakarun turai shi ne, idan har mu ka yi nasarar lashe gasar Premier, to mune zamu zamo kan gaba a karo na gaba."