Chelsea da Southampton sun tashi 1-1

Chelsea_Southampton Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Chelsea tana matsayi na daya a teburin Premier da maki 64

Chelsea da Southampton sun raba maki dai-dai a tsakaninsu, bayan da suka tashi kunnen doki a Stampord Bridge ranar Lahadi.

Diego Costa ne ya fara ciwa Chelsea kwallo da kai, daga baya Dusan Tasic ya farke da bugun fenariti.

Golan Southampton Fraser Forster ya hana kwallaye da dama shiga ragarsa, musammam kwallayen da Oscar da Eden Hazard da Loic Remy suka yi ta kai masa hari.

Har yanzu Chelsea tana matsayinta na daya a teburin Premier da maki 64 da kwantan wasa guda, ta kuma bai wa Manchester City tazarar maki shida.