Manchester United ta doke Tottenham 3-0

Manchester United_Tottenham
Image caption United tana mataki na hudu a teburin Premier biye da Arsenal mai matsayi na uku

Kungiyar Manchester United ta casa Tottenham da ci 3-0 a gasar Premier wasan mako na 29 da suka kara a Old Trafford ranar Lahadi.

Maroune Fellaini ne ya fara cin kwallo, daga baya Michael Carrick ya kara ta biyu, sannan Rooney ya kara ta uku.

Da wannan nasarar United tana mataki na hudu da maki 56 a teburin Premier, a inda ya rage maki biyu tsakaninta da Manchester City wacce take matsayi na biyu.

Tottenham tana mataki na bakwai a teburi biye da Southampton wadan da suke da maki 50 kowannensu.