Real Madrid ta doke Levente da ci 2-0

Real Madrid_Levente Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Madrid tana mataki na biyu a teburin La Liga da maki 64

Real Madrid ta hada maki uku, bayan da ta doke Levente da ci 2-0 a gasar La Liga wasan mako na 27 da suka kara ranar Lahadi.

Gareth Bale ne ya fara zura kwallo a raga a minti na 18 da fara wasa, sannan ya kara ta biyu saura minti biyar a tafi hutu.

Kwallayen da Bale ya ci ya kawo karshen kamfar cin kwallo a wasanni takwas da ya buga wa Madrid wasanni a baya.

Da wannan nasarar da Madrid ta samu ya sa tana mataki na biyu a kan teburin La Liga da maki 64, da tazarar maki daya tsakaninta da Barcelona wacce take matsayi na daya.