Van Gaal ya ba ni dama a United — Young

Van Gaal_Young Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption manchester United tana matsayi na hudu a teburin Premier

Ashley Young ya ce kociyan Manchester United Louis van Gaal ne ya taimaka masa a wasanninsa har ma ya ke sa ran Ingila za ta iya gayyatarshi.

Van Gaal, yana saka Young mai shekaru 29, a baya ko kuma a gaba ta bangaren hagu a gefe a wasannin United a bana.

Rabon da Young ya buga wa Ingila wasanni tun karawa da suka yi da Ukraine a watan Satumbar 2013, ya kuma buga wa kasarsa wasanni sau 30.

Kociyan Ingila Roy Hodgson ya halarci karawar da United ta casa Tottenham da ci 3-0 a gasar Premier ranar Lahadi a Old Trafford.