Sunderland ta kori Gus Poyet

Gus Poyet Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sunderland tana mataki na 17 a teburin Premier

Sunderland ta kori kocinta, Gus Poyet, bayan ya gaza tabuka komai tun da ta dauke shi aiki.

A baya bayan nan dai Poyet ya ci wasa daya ne kacal cikin wasanni 12 da ya jagoranci kungiyar.

Shugaban kungiyar, Ellis Short ne ya bayar da sanarwar korar kocin a inda ya kara da cewar "Mun tsinci kanmu cikin mawuyacin hali a gasar Premier da ya zama wajibi mu kawo sauyi."

Kungiyar ta sha kashi a hannun Aston Villa da ci 4-0 a gasar Premier ranar Lahadi, lamarin da ya sa ta koma mataki na 17 a teburin Premier da kuma maki 26.

Sunderland za ta ziyarci West Ham a wasan hamayya ranar Asabar a gasar Premier, sannan ta fafata da Newcastle ranar 5 ga watan Afirilu.