Liverpool ta doke Swansea da ci 1-0

Liverpool Team Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Liverpool za ta karbi bakuncin Manchester United ranar Lahadi

Liverpool ta doke Swansea har gida da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 29 da suka kara ranar Litinin.

Swansea ta kai hare-hare da dama kafin a tafi hutun rabin lokaci, a inda golan Liverpool Simon Mignolet ya hana kwallayen da Bafetimbi Gomis da Gylfi Sigurdsson suka buga masa shiga raga.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Liverpool ta sauya salon wasanta, wanda hakan ya sa ta zura kwallo a raga ta hannun Jordan Henderson a minti na 68.

Liverpool tana mataki na biyar a teburin Premier da maki 54, za kuma ta karbi bakuncin Manchester United wacce ke matsayi na hudu da maki 56 a ranar Lahadi