Sunderland ta nada Advocaat a matsayin koci

Image caption Tsohon kocin Netherlands

Sunderland ta na da Dick Advocaat a matsayin sabon manajan tawagar 'yan kwallonta har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Tsohon kocin Netherlands din ya kama aiki kwana guda bayan korar Gus Poyet.

"Burinmu daya ne, kawai mu haye saman tebur, kuma kowa ya sa ido a kan haka," in ji Shugaban Sunderland Ellis Short.

Advocaat mai shekaru 67 ya ce "Na kosa in soma aiki."

An kori Poyet ne bayan ya samu nasara a wasa daya cikin wasanni 12 a gasar Premier, wacce ke matakin na 17 a kan jadawalin gasar Premier, maki daya a saman kungiyoyin da za su nitse.