An cire Arsenal a gasar zakarun Turai

Arsene Wenger
Image caption Wannan ne karo na biyar a jere da Arsenal ta kasa kai wa wasan daf da na kusa da karshe

Arsenal ta kasa kai wa wasan daf da na kusa da karshe a gasar kofin zakarun Turai, duk da doke Monaco 2-0 da ta yi a Faransa ranar Talata.

Wannan ne kuma karo na biyar a jere da Arsenal ta kasa kai wa wasan daf da na kusa da karshe a gasar kofin zakarun Turai.

Arsenal ta zura kwallayenta biyu ta hannun Olivier Giroud da kuma Aaron Ramsey, jumullar kwallaye 3-3 a tsakaninsu.

Sakamakon doke Arsenal da Monaco ta yi da ci 3-1 a Emirates ne a karawar farko ya hana Arsenal kai wa wasan gaba a gasar.