Enyeama zai buga wa Nigeria wasa na 100

Vincent Enyeama Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Enyeama yana buga wasa a kulob din Lille ta Faransa

Mai tsaron gidan Super Eagles Vincent Eayeama, zai buga wa Nigeria wasa na 100, a karawar da Nigeria za ta buga wasan sada zumunta da Bolivia.

Enyeama mai shekaru 32, yana daga cikin 'yan wasa 28 da kociyan rikon kwarya Daniel Amokachi ya gayyato.

Sauran 'yan wasan da aka gayyata sun hada da Brown Ideye na West Brom da kuma Odion Ighalo mai wasa a Watford.

Shi ma dan kwallon Stoke City Victor Moses wanda ya ji rauni, yana daga cikin 'yan wasan da aka bai wa goron gayyata.

Nigeria za ta kara da Bolivia a ranar 26 ga watan Maris, daga nan kuma ta buga wani wasan da za ta ziyarci Afirka ta kudu ranar 29 ga watan Maris.