Giresse ya sake zama kociyan Mali

Alain Giresse Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne karo na biyu da kociyan zai horar da Mali

Mali ta sake daukar tsohon dan kwallon Faransa Alain Giresse a matsayin sabon kocin tawagar 'yan wasan kwallon kafarta a karo na biyu.

Kocin mai shekaru 62 da haihuwa, ya maye gurbin Henry Kasperczak, wanda ya ajiye aiki, bayan da kasar ta kasa kaiwa wasan zagaye na biyu a gasar kofin Nahiyar Afirka.

Giresse, wanda ya jagoranci Senegal a gasar kofin Afirka da aka kammala a Equatorial Guinea, bai kai kasar wasan zagaye na biyu ba a gasar.

Kocin ya jagoranci Mali kaiwa matsayi na uku a Gasar Kofin Afirka a shekarar 2012, lokacin da ya fara horar da tawagar kasar.