'Bai kamata Monaco ta fitar da mu ba'

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Arsenal tana mataki na uku a teburin Premier bana

Kociyan Arsenal Arsene Wenger ya ce bai cancanci ace Monaco ce ta cire su daga Gasar Kofin Zakarun Turai ta bana ba.

Wenger ya ce "Mun samu damar da za mu cire su a gasar a karo na biyu da muku buga a Faransa, domin ba su kai mana hari ko sau daya ba"

Monaco ta kai wasan daf da na kusa da karshe ne a gasar, bayan da ta doke Arsenal da ci 3-1 a wasan farko da suka kara a Emirates, sannan aka doke ta 2-0 a Faransa.

Kocin ya kara da cewa sun yi bakin cikin kasa kaiwa wasan gaba a gasar, amma ya yi murna da yadda 'yan wasansa suka taka leda.