Barcelona ta fitar da City a kofin Turai

Barcelona Manchester City Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Manchester City tana mataki na daya a teburin Premier

Barcelona ta fitar da Manchester City daga gasar cin kofn Zakarun Turai, bayan da ta doke ta da ci daya mai ban haushi ranar Laraba.

Barcelonar ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar, inda ta ci kwallonta ta hannun Ivan Rakitic daga tamaular da Messi ya ba shi.

Tun a karawar farko da suka buga a Ettihad Barcelona ce ta doke City da ci 2-1 a wasan farko da suka yi.

City ce kungiya ta hudu ta karshe daga Ingila da aka fitar daga gasar bana, a inda Liverpool da Chelsea da kuma Arsenal suka yi ban kwana tun farko.