Pellegrini ya tsinci dami a kala — Mancini

Manuel Pelegrini Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester City tana matsayi na biyu a teburin Premier

Roberto Mancini ya ce kociyan Mancheter City Manuel Pellegrini ya gaji kwararrun 'yan wasa a wajensa, wanda ya kamata ya dunga lashe kofuna a kowacce shekara.

Mancini ya fadi hakan ne a wata kafar yada labarai, inda ya kara da cewar kociyan ya yi sa a domin ya karbi ragamar horar da kulob din tare da fitattun 'yan wasa kwallon kafa.

City tana matsayi na biyu a teburin Premier, kuma za ta kara da Barcelona wacce ta doke ta 2-1 har gida a gasar Kofin Zakarun Turai wasan farko.

Mancini wanda City ta sallama a shekarar 2012 bayan da ya lashe kofin Premier, yanzu yana horar da Inter Milan ta Italiya.