Tsaro: Bolivia ta fasa karawa da Nigeria

Image caption Hukumar kwallon kafa ta Nigeria ta nuna rashin jin dadinta kan fasa zuwa kasar da Bolivia ta yi don buga wasan zumunci

Bolivia ta fasa zuwa Nigeria domin karawa da kungiyar kwallon kafa ta kasar a wasan sada zumunci da za su yi saboda dalilai na rashin tsaro.

An shirya za a buga wasan ne a garin Uyo da ke kudancin kasar saboda zaman lafiyar da ke yankin, da kuma nisan da ya yi da yankin arewa maso gabashin kasar wanda ake fama da tashe-tashen hankula.

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Bolivia Carlos Chavez ya ce "Irin rikicin da ake samu na kashe-kashen rayuka da yanayin siyasar da ake ciki na zaman dar-dar a kasar ne suka tirsasa mu janyewa daga buga wasan."

Hukumar kwallon kafa ta Nigeria ta bayyana lamarin da cewa abu ne ya zo mata da bazata ta kuma kasa amince wa da shi.

Hukumar ta kuma ce an sanar da FIFA halin da ake ciki.

A yanzu dai Nigeria tana neman kasar da za ta maye gurbin Bolivia domin buga wasan.