Wace gasar kwallon kafa ce tafi fice a duniya ?

Kasancewar kungiyoyin Ingila sun kasa yin abin azo a gani a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, BBC ta yi duba na tsanaki kan kasar dake kan gaba wajen yawan mabiya gasar wasanninta, wacce ce tafi taurarin 'yan wasa, a wace gasar aka fi kashe kudade, da wacce aka fi lashe kofuna da kuma yin gumurzu a wasanninta. A bangarenka wacce ce ke kan gaba.

Masu fadin magana sun ce kudi ba zai iya saya maka farinciki ba. A fannin taka leda baka da tabbacin za ka kai da yin nasara.

Wannan darasin ne gasar Premier Ingila ta fuskanta, duk da cewar itace gasar da kungiyoyinta suka fi arziki aka kuma fi kallon wasanninta a duniya, da kuma ikrarin da tayi cewar gasar ce tafi zan hankali a duniya.

Babu kungiyar Ingila da ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar kofin zakarun Turan bana, gasar da ita ce ta farko ta kungiyoyin kwallon kafa a duniya.

Wannan ne karo na biyu da hakan ta sake faruwa a cikin shekaru uku, wannan ne ya sanya shakku da alamar tambaya kan martabar Premier da tsakaninta da abokan hamayyarta La Ligar Spaniya da Bundesligar Jamus da Serie A Italiya.

Shin a ina ne aka fi murza leda mafi kayatarwa ne a duniya, kuma wace gasa ce ba tare da tantama ba ta fi yin fice ne a duniya.

Domin amsa wadan nan tambayoyin BBC ta auna da kuma kwatanta gasar manyan kasashe hudu, amma ba ta yi la'akari da salon tamaular da suke buga wa. Ga sakamakon binciken.

KOFUNA

Spaniya ba ta da abokiyar hamayya a wannan sashin, domin a shekaru 15 da suka ce kasar ta samu gagarumar nasara a daukar kofunan gasar Turai.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Banbancin lashe kofunan gasar nahiyar Turai da Spaniya ta dauka a kwai tazara mai yawa, domin ya fi jumullar kofunan da kasashe uku suka lashe. Real Madrid da Barcelona kowacce ta dauki kofin Zakarun Turai sau uku, Sevilla ta lashe kofin Uefa da Europa League, Atletico Madrid ta dauki kofin UEFA a inda Valencia ta lashe guda daya.

Ingila ce a matsayi na biyu, a inda ta dauki kofin zakarun Turai uku a shekaru 15 da suka wuce, inda Manchester Unite da Liverpool da kuma Chelsea suka lashe, kuma biyu daga cikinsu suka kuma dauki kofin UEFA.

Italiya ta dauki kofuna uku a inda AC Milan ta lashe biyu, Inter Milan ta dauki daya, yayin da Jamus ta lashe kofunan zakarun Turai biyu a shekaru 15 da suka wuce, kuma Bayern Munich ce ta dauki kofunan a shekarar 2001 da kuma 2013.

Idan muka yi waiwaye a karni na shekarar 1990, lokacin da Italiya ce ta mamaye lashe kofunan Turai inda ta dauki UEFA Cup guda uku da kofin zakarun Turai da kuma Uefa Cup guda bakwai.

Irin wannan sauyin kan haska makomar kasashen wajen dare matsayi na daya kan kasar da ta fi yin fice a Turai da Spaniya ce jagaba sai Ingila sannn Jamus a inda Italiya ke mataki na hudu.

Laliga tana da maki biyar, Premier nada mako uku, Serie A na da maki 2 sai Bundesliga wacce ke da maki daya.

ZAFIN GASA

Koci Jose Mourinho ya taba cewa yana matukar kauna gasar kwallon Birtaniya saboda yadda gasar take da zafi da kuma hamayya da ake tsakanin kungiyoyi da dama, kuma kowacce kungiya za ta iya lashe wasa.

A takaice ya zamo ruwan dare a gasar Spaniyar La Liga kungiyoyi biyu ne ake jin amonsu wato Real Madrid da Barcelona.

Wani abin sha'awa, a lokacin da Mourinho yake horar da Madrid ne ta yi rashin nasara a wasan karshe a Copa del Rey a hannun Atletico Madrid wacce ta dauki kofin La Liga a shekarar.

Sai dai kuma idan ka cire manyan kungiyoyin biyun Spaniya, kasar ce ke samar da yawancin kungiyoyin da ke tabuka rawar gani a gasar kofin zakarun Turai. A kalla kungiya daya kan shiga jerin teburin manyan kungiyoyi dake kan gaba a gasar.

Jamus tana da 11, Italiya na da 10.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A ingila. Kungiyoyi bakwai ne ke samun damar kai wa cikin jerin teburin manyan kungiyoyin da suka fi yin fice a gasar kofin zakarun Turan.

Tsohon mai tsaron bayan tawagar kwallon kafar Ingila Danny Mills ya bayyana gasar Premier da cewa gasa ce mai kayatarwa.

Ya kara da cewa "gasa ce da ake kallonta a fadin duniya kuma akoda yaushe ake sha'awa, kananan kungiyoyi kan doke manyan, abin da ya banbanta da sauran wasanni."

idan cin kwallo ne ke kawata gasa, to gasar Bundesliga ce a gaba, domin a kalla anci kwallaye uku a wasa a kakar wasan 2013-2014.

Sauran wasannin anci kwallaye 2.7 a wasa

Bundesliga nada maki 5, La Liga maki 3. Serie a maki 2, Premier maki 1

MABIYA

'Yan kallo ne suka kara karfafa gasar Bundesliga, domin 'yan kallo matsakaita 42,609 ke kallo wasa, hakan yasa ta rike mataki na biyu kuma biye da gasar kwallon zari rugar Amurka wacce tafi samun yawan 'yan kwallo a duniya a tarihin wasanni.

Akwai batutuwan da suka jawo haka

Jamus ce ke da yawan masu shiga kallon wasan kwallon kafa, amma ta saka 'yan kallon kwallon kasar cikin matsi, domin kulob ne ke daukar kaso 50 da daya cikin dari wajen shiga kallon wasa.

Haka kuma gasar Bundesliga ce ke da matsakaicin kudin tikitin kallon wasa a mafi arha a nahiyar Turai.

Wani bincike da BBC ta yi, ta gano cewar idan za ka kalli wasan Bayern Munich daga tsakanin dalar Amurka 15 zuwa 80 sai ka biya tikin kallon Arsenal daga dalar Amurka 40 zuwa 140.

A kasar Italiya da Spaniya kudin shiga kallon wasanni ya fi yawa. Kujerar kallon wasa a San Siro ta kama daga dalar Amurka 470 wasan AC Milan ko dalar Amurka 310 wasan Inter Milan, yayin da ake biyan dalar Amurka 293 kallon wasan Real Madrid da kuma dalar Amurka 243 a kallon wasan Barcelona.

Wannan farashin tikitin wasannin ya shafi masu sha'awar halartar kallon kwallon kafa. Bayan da aka fi shiga kallon Bundeslia, sai kuma gasar Premier da a takaice akan samu 'yan kallo 36,695 a wasa, sai gasar La Liga da ake samu 'yan kallo 26,955 a wasa.

Gasar Italiya wacce ta taba yin fice a duniya tana samun masu shiga kallon wasa 23,385 a wasa a tsawon kakar wasa, kasa kenan da mutane miliyan biyar da suke kallon Premier.

Bundesliga maki 5, Premier maki 3, La Liga maki 2, Seria A maki daya.

KUDADE

Ko shakka babu a nan ne gasar Premier ce kan gaba.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Wata daya da ya wuce aka cimma yarjejeniyar sayar da nuna wasannin gasar Premier kakar wasan 2016 zuwa 2019.

Sky Sports da BT za su biya dalar Amurka miliyan 7 da dubu 700 domin samun mallakar izinin nuna Premier, samun karin kaso 50 cikin dari na kudin shiga a shekaru uku daga kakar wasan 2013 zuwa 2016.

Kudin da kungiyoyin Premier za su samu yasa jaridar Deloitte ta saka kungiyoyin Premier cikin jerin masu arziki, a inda kungiyoyin Premier suka mamaye gurabe 14 daga cikin 30.

Tattalin arziki ya karawa kwallon kafa Ingila martaba a lokacin da aka yi musayar 'yan wasan kwallon kafa a shekarar 2014, a inda aka yi cinikayyar 'yan wasa da ta kai dalar Amurka miliyan dubu daya da 200, karin kaso 67 daga cikin dari fiye da hadahadar da aka yi a Spaniya.

A cewar rahoton baya bayan nan kan kashe kudi da kafar yada labarai ta TV Sports ta fitar akan kwallon kafa, Seria a ce ke mataki na biyu kan kashe kudin masayar 'yan kwallo da ya kai dalar Amurka miliyan dubu daya.

La Ligar Spaniya ta hada kasa da dalar Amurka miliyan 900, kuma shima kokari ne da wasu kungiyoyi suka yi kan tallata wasanninsu maimakon jumullar kungiyoyin.

An yi hada hadar cinikin 'yan wasa a Bundesliga da ta kai dalar Amurka 570, kuma wannan kudi ya wakilci kaso 54 cikin 100 fiye da kwantiragin da suka cimma a baya.

Premier League maki 5, Serie A, maki 3, La Liga, maki 2, Bundesliga maki 1.

BAYANAI

Spaniya ta mamaye wasannin bana, a inda Real Madrid take da tana da dan wasa Cristiano Ronaldo yayin da Barcelona ke da Lionel Messi, kuma dukkansu sun nuna kansu a matsayin 'yan wasan da suka fi yin fice a duniya.

'Yan wasan biyu sun zura kwallaye 102, Messi ya ci 50, Ronaldo ya zura 52, a tsakaninsu a shekaru biyar da suka wuce a gasar zakarun Turai, kuma sun lashe kyautar gwarzon dan wasan da yafi yin fice a duniya a shekaru bakwai da suka shude.

Manyan kungiyoyin La Liga suna da 'yan wasan da aka fi saye da tsada a tarihi a duniya da suka hada da Gareth Bale da Ronaldo da Luis Suarez da Neymar da kuma James Rodriguez.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Premier tana mataki na shida, a inda ta dauko dan kwallon Argentina Angel Di Maria. Italiya tana matsayi na 18 a inda Jamus ke mataki na 18.

Cikin 'yan wasa 16 da aka saya mafi tsada a duniyan, Spain tana da 'yan wasa uku, Birtaniya nada 10, sai kasar Faransa albarkacin kulob din PSG da Monaco wacce keda 'yan wasa bakwai, Italiya nada uku Jamus da Rasha suna da bibiyu kowannensu.

La Liga maki 5, Premier League maki 3, Bundesliga maki 2, Series A maki 1.

SAKAMAKO

La Liga, Spain, maki 17 Premier League, Ingila maki 15 Bundesliga, Jamus maki 14 Serie A, Italiya maki 9.