Blatter ya ki amincewa da tayin muhawarar talabijin

Sepp Blatter Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Blatter yana neman shugabancin FIFA karo na biyar

Sepp Blatter yaki amincewa da tayin da BBC da Sky suka yi masa na tafka muhawara tsakanin 'yan takarar kujerar FIFA.

Muhawarar da BBC da Sky suka yi wa Fifa ta yi, za ta kunshi yin tambayoyi daga ma'abota kwallon kafa da za su yiwa 'yan takara.

Ranar 29 ga watan Mayu a Zurich ake sa ran zaben shugaban hukumar Fifa, inda Sepp Blatter yake fatan a zabe shi karo na biyar.

Sauran 'yan takarar kujerar Fifa sun hada da Yarima Ali Bin Al Hussein na Jordan da Michael van Praag na Netherlands da kuma Louis Figo na Portugal.