Mourinho ya yi korafi kan fenariti

Diago Costa Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea tana mataki na daya a teburin Premier

Kociyan Chelsea Jose Mourinho ya ce hana fenariti da ake yi a Premier bana ya yi karanci idan aka auna da wadan da aka bayar a kakar bara.

A wata kididdiga da kulob din ya rubuta a shafinsa na Intanet, ya ce sau biyu kawai aka bai wa Chelsea fenariti a bana, inda aka bai wa Arsenal da Manchester City bakwai kowannensu.

Fenaritin da aka bai wa Chelsea a bana sun hada a karawa da Arsenal a Oktoba da kuma a wasa da QPR a watan Nuwamba.

A watan Janairu sai da FA ta ci tarar Mourinho, bisa ikirarin da ya yi cewar alkalin wasa sun game kansu domin durkusar da Chelsea.

A kakar wasannin bara sau bakwai aka bai wa Chelsea fenariti.