Za a buga kofin duniya a Qatar a Disamba

Qatar 2022
Image caption Za a fara gasar kofin duniya a shekarar 2022 ranar 18 ga watan Disamba

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta tabbatar da cewar za a fara buga gasar cin kofin duniya a Qatar daga ranar 18 ga watan Disambar 2022.

Wani kwamitin da FIFA ta dorawa alhakin fitar da lokacin da ya kamata a buga gasar ne ya bayar da shawara sauya wasannin daga lokacin bazara zuwa hunturu.

Shawarar da aka yanke kan fara gasar kofin duniya ranar 18 ga watan Disamba, na nufin ba zai hana karawa a wasannin Premier da aka saba bugawa a lokacin ba.

Haka kuma an amince da zabar kasar Faransa ta karbi bakuncin gasar kofin duniya ta mata 'yan kasa da shekaru 20 a shekarar 2019.