Magoya bayan AC Milan sun kaurace wa wasa

Milan Fans Hakkin mallakar hoto epa
Image caption AC Milan tana mataki na 7 kan teburin Serie A

Dubban magoya bayan kulob din AC Milan ne suka kaurace wa karawar da ya yi da Cagliari a gida a gasar Seria A ranar Asabar.

Magoya bayan kulob din sun kaurace wa wasan ne domin bayyana fushinsu kan yadda shugaba Silvio Berlusconi ke gudanar da kulob din.

Sai dai kuma Milan ya samu nasara a karawar da ci 3-1, kuma nasarar ta sa ya koma mataki na bakwai a kan teburin Serie A.

Ba a fitar da adadin 'yan kallon da suka shiga filin wasa na San Siro mai diban mutane 80,000 a ranar Asabar ba, amma yawancin kujeru babu 'yan kallo.

AC Milan ya lashe kofunan Serie A 18, kuma ya kammala gasar bana a mataki na takwas dalilin da yasa ya kasa shiga gasar kofin zakarun Turai ta bana.