Gasar Premier bata da karsashi — Moyes

Messi Moyes Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Moyes ne ke horar da kulob din Real Sociedad na Spaniya

Tsohon kociyan Manchester United, David Moyes, ya bayyana gasar Premier bana da rashin karsashi tun lokacin da aka fara gasar a baya.

Kociyan da yanzu ke horar da Real Sociedad ya ce "Mun dade muna yayata ficen da Premier ta yi, amma gasar bata kai yadda muke tsammani ba".

Babu wata kungiya da ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar kofin zakarun Turai na bana, idan aka kwatanta da na Spaniya.

Kocin ya kuma soki gasar game da yadda ake kashe makudan kudi wajen dauko 'yan wasan kwallon kafa a duniya.