Heartland ta casa Nasarawa United 5-2

Enyimba Stadium Hakkin mallakar hoto enyimba stadium lmcnpfl twitter
Image caption An kammala wasannin mako na uku, sai wasan Pillars da kuma na Dolphins ya rage

Heartland ta doke Nasarawa United da ci 5-2 a gasar Premier ta Nigeria wasan mako na uku da suka kara ranar Lahadi.

Heartland ta ci kwallayenta ta hannun Ebere Odiche da Fred Okwara da Bright Ejike wanda ya ci kwallaye biyu da kuma Joseph Iniobong

Ita kuwa Nasarawa United ta farke kwallaye biyu ne ta hannun Mannir Ubale da kuma Mustapha Musa.

Sauran sakamakon wasannin Enyimba ta lashe Bayelsa United da ci daya mai ban haushi, ita ma Giwa FC daya mai ban haushi ta doke Sunshine Stars.

Karawar da aka yi a Kano Elkanemi ce ta casa Abia Warriors da ci 3-1, yayin da aka tashi wasa babu ci tsakanin Taraba United da Lobi Stars.

Ga sakamakon wasannin mako na uku da aka buga

Enyimba 1 vs 0 Bayelsa United FC Taraba 0 vs 0 Lobi Stars Gabros 1 vs 0 Rangers Giwa 1 vs 0 Sunshine Stars El-Kanemi Warriors 3 vs 1 Abia Warriors Heartland 5 vs 2 Nasarawa United