Messi ya fi Ronaldo fice a duniya -— Pele

Ronaldo Messi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Pele ya ce 'yan wasan biyu babu kamarsu, amma Messi ya fi fice

Tsohon dan kwallon Brazil Pele, ya ce Lionel Messi ne ya fi yin fice a iya taka leda a duniya fiye da Cristiano Ronaldo tun shekaru 10 da suka wuce.

Pele ya shaida wa BBC cewa "Jama'a na auna wanda ya fi kokari tsakanin Messi da Ronaldo, sai dai kuma sun bambanta a wajen salon murza leda".

Mai shekaru 74 da haihuwa ya kara da cewa " Dukkansu fitattun 'yan wasan kwallon kafa ne a duniya, amma a shekaru goma da suka wuce Messi ne ya fi yin fice".

Messi ya lashe kyautar gwarzon dan wasan da ya fi yin fice a duniya sau hudu, a inda Ronaldo ya karbi kyautar sau uku.

Haka kuma Ronaldo ya lashe kofunan Premier uku da Manchester United da La Liga a Madrid da kuma kofin Zakarun Turai a dukkan kungiyoyin biyu.

Shi kuwa Messi ya dauki kofunan La Liga shida da kuma na Zakarun Turai sau uku tare da Barcelona.