Za a takaita baki da ke buga Premier

Greg Dyke Hakkin mallakar hoto PA
Image caption FA tana son kawo cigaban 'yan wasan Ingila a Tamaula

Shugaban hukumar kwallon kafar Ingila Greg Dyke ya yi gargadi kan hatsarin da yake tunkarar wasan Premier, sakamakon karancin 'yan kasa dake buga gasar.

Hukumar ta mika bukatar takaita yawan 'yan wasan da ke buga Premier, wadanda ba sa cikin tarayyar Turai.

FA ta ce za ta kara tsaurarawa da kuma inganta dokar da ta kafa wadda ta bai wa kungiyoyi damar renon matasa 'yan wasan gida da aka kafa a shekarar 2013.

Haka kuma hukumar ta ce za ta sake bitar takardun bai wa 'yan wasa izinin shiga buga gasar, domin akwai kura-kurai da dama.