FA na binciken fada tsakanin Skrtel da De Gea

Skrtel De Gea Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption United tana matsayi na hudu a teburin Premier, Liverpool tana mataki na biyar

Hukumar kwallon kafar Ingila na nazari kan hayaniyar da ta barke tsakanin Martin Skrtel da David De Gea.

Lamarin ya faru ne a karawar da Manchester United ta doke Liverpool 2-1 a gasar Premier ranar Lahadi.

Alamu sun nuna cewa Skrtel dan kasar Slovakian mai shekaru 30, ya taka gola De Gea daf da za a tashi wasan da suka kara a Anfield.

FA ta ce tana duba yadda za ta gano mai laifi tsakanin 'yan wasan biyu, bisa yadda suka dinga mayar wa junansu maganganu bayan da aka ta shi wasan.

Haka kuma hukumar tana son ta gano idan alkalin wasa Martin Atkinson ya shaida abin da ya faru tsakanin 'yan wasan.