'Ina fargabar Dortmund za ta bar Bundesliga'

Borrusia Dortmund Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dortmund tana mataki na 10 a teburin Bundeslia

Kociyan Borussia Dortmund Jurgen Klopp ya ce ba zai daina fargabar watakila su bar buga gasar Bundesliga ba, har sai sun bar karshen teburi.

Dortmund ta doke Hannover ranar Asabar da ci 3-2, kuma nasarar lashe wasanni bakwai da ta yi a jere kenan, sannan ta koma mataki na 10 kan teburin Bundesliga.

Rabon da a doke Dortmund tun ranar 4 ga watan Fabrairu a lokacin da ta kara da Augsburg, bayan fafatawar ne 'yan wasa suka bai wa magoya baya hakuri.

A watan Fabrairun bara Dortmund ce ta karshe a teburin Bundesliga, amma yanzu ta koma mataki na 10.