Simeone ya tsawaita kwantiragi a Atletico

Diego Simeone Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Diego Simeone ya fara horar da Atletico a shekarar 2011

Kociyan Atletico Madrid Diego Simeone ya tsawaita kwantiraginsa a Atletico Madrid zuwa shekarar 2020.

Simeone -- mai shekaru 44 -- ya jogoranci Atletico wajen lashe kofuna da dama tun lokacin da ya zama kociyan kulob din a shekarar 2011.

Cikin kofin da Atletico ta dauka har da na La Liga da na Europa League, sannan ta zamo ta biyu a gasar cin kofin zakarun Turai a shekarar 2012.

An hakikance cewar Simeone yana daga cikin fitattun masu horar da ‘yan wasan kwallon kafa a Turai, har ma ana rade-radin cewa zai zama kociyan Manchester City.