Kofin duniya 2026: Ingila za ta nemi bakunci

German Team Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rasha ce ta doke Ingila a neman bakuncin gasar 2018.

Shugaban hukumar kwallon kafar Ingila, Greg Dyke, ya ce watakila Ingila ta nemi izinin karbar bakuncin Gasar cin Kofin Duniya ta shekarar 2026.

Sai dai kuma shugaban ya ce hakan ya danganta da sake zaben Sepp Blatter a matsayin shugaban Fifa karo na biyar da kuma wadansu dalilai.

Ya kuma kara da cewar zaben dan kasar Ingila David Gill da aka yi a cikin manyan jami'an FIFA zai taimakawa kasar cimma burinta.

Rasha ce ta doke Ingila a zaben neman izinin karbar bakuncin kofin duniya na shekarar 2018, a inda ta kare a mataki na hudu da kuri'u biyu kacal.

An kafa kwamitin bincike kan Rasha da Qatar saboda yadda suka samu damar karbar bakuncin gasar 2018 da kuma 2022 wadda ke cike da zargin cin hanci da rashawa.