FA tana tuhumar Skrtel da yin keta da gangan

Martin Skrtel Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption FA ta bai wa Skrtel damar ya kare kansa daga tuhumar da ake yi masa

Hukumar kwallon kafar Ingila tana tuhumar Martin Skrtel da yi wa Golan Manchester United David De Gea keta da gangan.

Lamarin ya faru ne daf da za a tashi a karawar da Manchester United ta doke Liverpool da ci 2-1 a gasar Premier a Anfield ranar Lahadi.

An bai wa dan wasan dan kasar Slovekia mai shekaru 30, nan da zuwa ranar Talata da yammaci ya kare kansa ko kuma a dakatar da shi daga buga wasanni uku.

Alkalin wasa Martin Atkinson bai ga lokacin da Skrtel ya yi ketar ba, amma mataimakansa sun hakikance cewar laifin da yayi, ya kamata a kore shi daga wasan.

Alkalan sun cimma wannan matsayar ne, bayan da suka kalli laifin da dan wasan ya yi ta akwatin talabijin.

Idan har Skrtel bai kare kansa daga tuhumar da FA take yi masa ba, to ba zai bugawa Liverpool wasannin da za ta buga da Arsenal da Newcastle a gasar Premier da kofin Kalubale da Blackburn ba.