Gill ya lashe zaben mataimakin shugaban FIFA

David Gill Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gill shi ne mataimakin shugaban hukumar kwallon kafar Ingila

Tsohon jami'in Manchester United, David Gill, ya lashe zaben mataimakin shugaban FIFA daga nahiyar Turai.

Gill, mataimakin shugaban hukumar kwallon kafar Ingila, wanda zai fara aiki a watan Mayu, ya yi takarar mukamin ne tare da shugaban hukumar yankin Wales Trefor Lloyd Hughes.

Ya lashe zaben ne da kuri'u 43 daga cikin 53 da aka kada, zai kuma maye gurbin Jim Boyce na Ireland ta Arewa.

Sai dai yankin Wales ya zargi Ingila da yankan baya, ganin cewa a baya sun cimma yarjejeniya cewa za su dinga juya mukaman a tskanin kasashe hudu.

Gill ya ce tun a baya an rushe yarjejeniyar, tun lokacin da FIFA ta ce za a dinga yin zaben ne tsakanin mambobin hukumar kwallon kafar duniya.