Platini na tsoron karuwar 'yan daba a filayen wasa

Michael Platini Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Platini zai jagoranci hukumar kwallon Turai karo na uku

Michael Platini ya yi gargadin cewa za a iya samun karuwar rikice-rikice a filayen wasan, kamar yadda aka sha fama a baya.

Platini ya yi gargadin ne a lokacin da aka sake zaben shi a matsayin shugaban hukumar kwallon kafar Turai a karo na uku a jere.

Ya kuma kara da cewa ana ta samun karuwar tashe-tashen hankali a filayen wasan daban-daban.

Ya kuma yi kira da a samar da 'yan sandan kwantar da tarzomar wasanni a nahiyar Turai wadanda za su dinga sa ido a lokutan wasanni.

Platini ya buga wa Juventus a karawar da suka yi da Liverpool a shekarar 1985 a wasan karshe na cin kofin Zakarun Turai lokacin da 'yan kallo 39 suka mutu sakamakon barkewar tarzoma a filin Heysel.