Petr Cech zai bar Chelsea a badi

Petr Cech Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cech ya koma Chelsea a shekarar 2004, kuma wasanni 11 ya buga a bana

Golan Chelsea, Petr Cech, ya ce yana duba yiwuwar barin kulob din a karshen kakar wasa ta bana, domin ba zai iya zaman dumama benci ba.

Wata majiyar da ke kusa da golan wanda ya koma Chelsea a shekarar 2004 ta shaida wa BBC cewa dan wasan ya ce yana son ya dinga buga wasanni akai-akai.

Cech, ya buga wa Chelsea wasanni 14 a kakar wasan bana, a inda Thibaut Courtois ya maye gurbinsa a matsayin babban gola.

Golan wanda zai buga wa Jamhuriyar Czech wasa a ranar Juma'a, ana rade-radin zai koma taka leda a Arsenal ko kuma Liverpool.