Falcao na son buga wasa a United akai-akai

Radamel Falcao Hakkin mallakar hoto AP
Image caption United tana mataki na hudu a teburin Premier

Radamel Falcao wanda ke wasa aro a Manchester United ya ce yana son a dinga saka shi a wasa akai-akai idan har ana son ya ci gaba da zama a kulob din.

Dan kasar Colombia, mai shekaru 29, ya zura kwallaye hudu daga cikin wasanni 22 da ya buga wa United tun komawarsa kulob din aro daga Monaco.

Rabon da Falcao ya buga wasa tun lokacin da United ta doke Sunderland da ci 2-0 a gasar Premier ranar 28 ga watan Fabrairu.

Tsohon dan kwallon Porto da Atletico Madrid ya ce yana samun kungiyoyin da ke zawarcinsa, amma a yanzu ya kwantar da hankalinsa har zuwa karshen kakar wasan bana.