Vermaelen ya koma atisaye da Barcelona

Thomas Vermaelen Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona tace dan kwallon zai fara buga mata wasa a watan gobe

A karon farko Thomas Vermaelen, ya yi atisaye tare da abokan wasansa a Barcelona, tun bayan da likitoci suka yi masa aiki a watan Disamba.

Dan kwallon Belgium mai shekaru 29, kuma tsohon dan wasan Arsenal, har yanzu bai buga wa Barcelona tamaula ba, sakamakon raunin da ya ji a gasar kofin duniya a Brazil.

Barcelona ta sanar a shafinta na internet cewa tana fatan Vermaelen zai fara buga mata wasanni a watan gobe.

Vermaelen ya fara buga tamaula a Ajax, daga nan kuma ya koma Arsenal a inda ya buga wasanni tsawon shekaru biyar kafin ya koma Barca.