Terry ya sabunta kwantiraginsa a Chelsea

John Terry Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Chelsea ta tsawaita kwantiragin Terry zuwa shekara daya

John Terry ya sabunta kwantiraginsa da kulob din Chelsea zuwa karshen kakar wasanni ta 2015-16.

Kyaftin din, Chelsea mai shekaru 34, kwantiraginsa zai kare da kulob din a karshen karar wasanni ta bana.

Terry, wanda ya koma Chelsea daga West Ham a shekarar 1998, ya buga wasanni 445 kuma ya ci kwallaye 37.

Chelsea ce ke kangaba a teburin Premier da maki 67 da kwantan wasa guda, a inda ta bai wa Manchester City mai matsayi na biyu tazarar maki shida.