NFF ta sabunta kwantiragi da Keshi

Stephen Keshi
Image caption Super Eagles bata kare kofinta a Equatorial Guinea ba

Shugaban hukumar kwallon kafa na Nigeria Amaju Pinnick ya ce Stephen Keshi zai ci gaba da horar da tawagar kwallon kafar kasar.

Keshi mai shekaru 53, wanda ya jagoranci Super Eagles ta lashe kofin Nahiyar Afirka a shekarar 2013, an sabunta kwantiraginsa zuwa shekaru biyu.

Tun farko kwantiragin kociyan ya kare da Super Eagles ne bayan kammala gasar kofin duniya a Brazil, a inda Nigeria ta kai wasan zagaye na biyu.

Pinnick ya ce "Ranar Laraba ne kwamitin amintattu na NFF ya amince da shawarar da kwamitin tsare-tsare ya mika masa cewar Keshi ya ci gaba da jagorantar Super Eagles".

Tun bayan da Nigeria ta kasa shiga gasar kofin Afirka a 2015 domin kare kambunta, aka samu rarrabuwar kawuna akan ko ya kamata a cigaba da barin Keshi ya horar da kasar.