Kungiyoyin gasar Premier za su raba fam biliyan daya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester City ce ta lashe kofin a bara

Kungiyoyin da ke buga gasar Premier ta Ingila sun amince su raba akalla fam biliyan daya na kudaden da suke samu daga nuna wasan a talbijin tare da kananan kulob-kulob na kasar.

Kudaden sun hada da alawus-alawus da za a dinga biyan kungiyoyin da za su daina buga gasar Premier su koma Championship.

Kungiyoyin Premier sun sayar da damar nuna wasanninsu kai tsaye a gidajen talbijin kan tsabar kudi fam biliyan 5.136 ga kamfanin Sky da kuma BT na tsawon shekaru uku daga shekarar 2016.

Kudaden shigar da suke samu sun karu da kashi 40 cikin 100 daga cikin fam miliyan 700 bayan da kudin da gidajen talbijin ke nuna wasannin ya karu da kashi 70 cikin 100 daga fam biliyan uku.

Shugaban gasar Premier ta Ingila Richard Scudamore, ya ce: "Wannan wani ci gaba ne da ba a taba samun irinsa a duniyar wasanni, balle a wasan kwallon kafa, hakan kuma zai samar da ci gaba na dogon lokaci a wasannin Ingila ko dai ga masu sha'awar wasan kwallo ko ga kananan kulob-kulob ko ga masu mu'amala da wasannin da ake yi a yankunan karkara."