Brook ya kare kambunsa ajin IBF

Brook Jo Jo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sau 34 kenan Brook yana lashe wasannin da ya yi

Kell Brook ya kare kambunsa na IBF ajin welterweight bayan da ya doke Jo Jo Dan a turmi na hudu a Sheffield.

Sau hudu Brook, dan kasar Ingila, yana kai Jo Jo dan kasar Romania kasa, kafin daga baya ya kasa tashi a turmi na hudu.

Rabon da Brook ya yi dambe tun a watan Agustan 2014 a California, lokacin da ya doke dan kasar Amurka, Shawn Porter.

Wannan ne karon farko da Brook, mai shekaru 28, ya kare kambunsa tun bayan da aka daba masa wuka a kafarsa, lokacin da yake yin hutu a Tenerife.