'Yan wasan Ingila hudu za su yi jinya

Danny Welbeck Hakkin mallakar hoto
Image caption Welbeck ya ji raunin ne a ranar Juma'a a wasa da Lithuania

Dan kwallon Arsenal Danny Welbeck ba zai buga wasan sada zumunta da Ingila za ta yi da Italiya a Turin a ranar Talata ba.

Welbeck, ya ji raunin ne a lokacin da yake buga wa Ingila wasan neman gurbin shiga gasar kofin nahiyar Turai da Lithuania ranar Juma'a, inda Ingila ta lashe wasan da ci 4-0.

Kociyan Ingila Roy Hodgson ya ce Welbeck zai yi jinya tare da dan wasan Liverpool Raheem Sterling da James Milner na Manchester City da dan kwallon Everton Leighton Baines.

Tuni kociyan ya gayyato dan wasan Southampton Ryan Bertrand domin maye gurbin Leighton Baines.