Toure zai yi ritayar buga wa kasarsa kwallo

Yaya Toure
Image caption Toure zai sanar da lokacin da zai yi titaya daga buga wa Ivory Coast kwallo

Dan kwallon Manchester City, Yaya Toure, ya ce zai sanar da shirinsa na yin ritaya daga buga wa Ivory Coast tamaula a cikin makon nan.

Toure shi ne ya jagoranci kasarsa lashe kofin nahiyar Afirka da aka yi a Equatorial Guinea wanda rabonta da daukar kofin tun a shekarar 1992.

Dan wasan ya kara da cewar lokaci ya yi da ya kamata ya bi sawun dan uwansa Kolo Toure wanda ya yi ritaya bayan kammala gasar kofin Afirka a bana.

Sai a shekarar 2017 ne kwantiragin Toure za ta kare da Manchester City, ya kuma ce zai mai da hankali wajen buga wa kulob dinsa wasanni.

Toure zai yi ritayar buga wa kasarsa kwallo