Zambia za ta sauya kociyanta Janza

Honour Janza Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kalusha ya ce Janza yana bukatar samun karin horo

Hukumar kwallon kafar Zambia ta tabbatar da cewar tana neman koci bature wan da zai maye gurbin kociyanta Honour Janza.

Shugaban hukumar kwallon kafar Zambia Kalusha Bwalya ne ya bayar da sanarwar, ya kuma kara da cewar Janza kociyan gida ne yana kuma da bukatar samun karin horo.

Zambia ta nada Janza a matsayin kociyan tawagar kwallon kafar kasar a watan Agustan 2014, a inda ya maye gurbin Patrice Beaumelle.

Kuma Janza ne ya jagoranci Zambia a gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka kammala a Equatorial Guinea a inda kasar ta kasa kaiwa wasan zagaye na biyu.

Haka kuma kungiyoyin Zambia sun ki amincewa da wata bukatar da aka mika wacce tace sai wanda ya yi aiki a cikin kwamitin amintattu na hukumar kwallon kafar kasar ne zai nemi takarar shugabancin hukumar da kudin sayen fom da ya kai dala 3,000.